<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>300</hymn_number>
<title>Salama Ta Allah Kamar Kogi Ce LW300</title>
<lyrics>[V1]
 1) Salama ta Allah kamar kogi ce.
 Tana ikon kome cikin yalwarta.
 Cikakkiya mai gudu, tana ƙaruwa,
 Cikakkiya mai girma kamar zurfafa.

[V2]
 KORUS
 Dogara ga Allah, hanyar kwanciyar  rai
 Gunsa za a sami hutu cikakke.

[V3]
 2) Daga tafin hannun Ubangijinmu,
 Ba abokin gaban da zai fizge mu.
 Babu tashin zuciya, babu damuwa,
 Babu kuwa dalilin tunani mai yawa.
 Korus</lyrics>
</song>